GIDAN RADIYON “rfi hausa” KUN YI MANA KARYA. TSAKANINMU DA KU ALLAH YA ISA”! “”””””””””””””””””””” #Murtadha_Yelwan_Shendam ===============

A cikin labaransu na 9:00pm. Yau Juma’a 12/1/2018, gidan Radiyon France rfi,

sun fada cewa;

Hukumomi a Nigeria sun karyata labarin Mutuwar Sheikh Zakzaky. Amma an sami Arangama tsakanin Jami’an Tsaro da masu Zanga-zangar a sako Sheikh Zakzaky, amma sai masu Zanga-zangar suka koma tayar da Tarzoma….. . Haba rfi hausa! Me ya sa ba za ku fadi alkhairi ba sai dai sharri? .

Daman wannan shi ne aikin Jarida? . A sanina dai shi dan Jarida rantsuwa ya yi a kan cewa zai fadi labarin gaskiya ba tare da goyon bayan wani bangare ba a yayin da yake gudanar da aikinsa. .

To shin meyasa ku ba za ku yi mana adalci fadi gaskiyar abun da ke faruwa da mu ba a cikin labaranku? .

Kullun muka fito Muzahara sai Jami’an Tsoro sun harharba mana Barkonon Tsohuwa da na Budurwa. Sai sun har bi ‘Yan uwanmu da Harsashi mai rai, wasu sun yi Shahada, wasu sun yi raunuka, wasu an kama su an je an azabtar da su, duk kuma kun san da wannan. An harbi Wakilin ‘yan uwa na Sokoto Malam Kasimu Umar an karya masa kafa, duk kun san da wannan. To meyasa ba za ku fada wa Duniya ba? . Ko da yake ba mu yi mamakin ku ba a kan haka, domin Muradin iyayen gidanku kuke karewa. Daman an samar da ku ne don ku yi wa Turawa da Yahudawa makiyan Musulunci da Musulmi aiki. . Ko a shekaranjiya laraba Munji Takwararku BBC hausa sun yi mana karyar da suka saba yi mana suka ce; an yi an yi arangama tsakanin ‘yansanda da mabiyan Zakzaky a Abuja lokacin da suke zanga-zanga a kan Gwamnati ta sako musu shugabansu, masu Zanga-zangar sun ce ‘Yan sandan sun harharbe su. Su kuma ‘yan sandan sun ce sun yi hakan ne saboda masu Zanga-zangar sun farfasa musu Motoci…. . . Abun mamaki, tun daga wancan Rahoton na BBC na ranar laraba har yau babu wata Tashar talabiji ko wata Jarida da ‘yan sandan suka nuna Motocin da suka ce wai an Farfasa musu. . To ku sani kullun kara zubar da mutuncinku kuke yi a wajen Jama’a, domin duk abun da kuke fada na karya a kanmu Duniya ta san karya kuke mana, domin motsin da muke yi ba a boye muke yi ba.

Duniya tana kallo, kuma duniya tana sane da irin kyakkyawar tarbiyar da Jagoranmu(H) ya ba mu. . A karshe nake cewa, duk Dan Jaridar da aka yi amfani da shi wajen yi mana sharri wallahi mun san shi. Mun san sunan shi da komai na shi, za mu sanya sunan shi a jerin sunayen da muke yi wa bakar Addu’a. Insha Allahu masu amfani da ku sune za su yi ajalinku. Daman Bature da Bayahude idan yai amfani da kai sai ya kashe ka. Ku jira lokaci na zuwa, daya bayan daya sai kun ga sakamakon aikinku tun a nan duniya. Kuma Wallahi ‘ya’yanku Shi’a za su yi. Kuma sai sun karanta tarihin Rayuwarku sun ga irin Miyagun ayyukan da kuka aikata a rayuwarku. .

Murtadha Yelwan Shendam

12/01/2018.

Hotuna ta’addancin abinda Jami’an tsaron Gwamnatin @MBuhari suke mana indan muka fito zanga-zangan ta Luma su na harba mana teagas da kuma harsasai da suke harbawa shike barfasa wa wasu motocin su.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s